
REVIVE THY WORK, O LORD
(HAUSA 249) |
YA YESU MAI CETO, KA BA NI SABON RAI
- Ya Yesu Mai Ceto, ka ba ni sabon rai,
Ka tsarkake ni da jininka, in ji, in bi sosai.
Korus:
Ka ba ni sabon rai, a cikin zuciyata
Ka sauko nan da ikonka, ka ba ni sabon rai!
- Ya Ruhu Mai Tsarki, farkad da ni yanzu
Daga nauyi, barci, ragwanci, ka wartsakad da ni.
- Uba, ina rokonka ka ba ni kishirwa,
Ka shayar da ni, da ruwa mai rai, ka amsa kukana.
- Yesu, Ruhu, Uba, na girmama ka yau.
Ka sauko nan da ikonka, na ba ka zuciyarta.
- Sai mu tashi fa ‘yanuwa, mu yi ta yin addu’a
Mu yi shelar Yesu da cetonsa da karfin zuciya.