Comments are off for this post

WANDA YA KE NEMAN CETO DAGA ZUNUBI [HAUSA VERSION]

WANDA YA KE NEMAN CETO DAGA ZUNUBI      

  1. Wanda yake neman ceto daga zunubi,

Wanda yake so ya daina nufin zunubi,

Ya zo ya ji labarin wani, shi Mai Cetonmu,

Sunansa Yesu ne.

 

Korus:

                    Yesu, Yesu ne Mai Ceto

                    Yesu, Yesu ne Mai Ceto

                    Yesu, Yesu ne Mai Ceto

                    Yesu, Mai Ceto ne.

 

  1. Ko ka yi kokari kome yawan famanka,

          Ba ka iya kome don ka ceci ranka ba,

Mai Ceto guda daya ne, tausayi gare shi kowa,

Sunansa Yesu ne.

 

  1. Zo ka kasa kunne ga jawabina yanzu,

Sai ka nemi ceto wurin Ubangijinmu,

Bari neman kowa sai Mai Cetonmu kadai,

Sunansa Yesu ne.

 

Comments are closed.