Comments are off for this post

YESU MU KE SO DON YA CECE MU [HAUSA VERSION]

RESTING ON THE EVERLASTING ARM

(HAUSA 224)

YESU MU KE SO DON YA CECE MU

  1. Yesu mu ke so don ya cece mu,

Muna jingina ga kirjinsa,

Shi ya mutu dai don mu sami rai,

Muna, murna cikin cetonsa.

 

Koros:

Yesu………. Yesu……………….

          Kaunar Yesu mai girma ce,

          Yesu……….. Yesu ………………

          Yesu ya mutu domin laifinmu.

 

  1. Yesu mu ke bi har mutuwarmu,

Muna dogara ga ikonsa,

Shi ya tsare mu daga mugunta,

Muna murna cikin kaunarsa.

 

  1. Shi mai ba da rai na har abada,

Muna jingina ga hannunsa,

Shi ya zabe mu daga duniya,

Muna murna cikin ikonsa.

Comments are closed.